Hezbollah ta samu 'yar galaba a kan 'yan tawaye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hezbollah na goyon bayan shugaba Assad

Mayakan Hezbollah tare da kawancen dakarun kasar Syria sun samu karin galaba kan 'yan tawaye a yankin nan mai tsaunuka da ke kan iyakar kasar da Lebanon.

Mayakan na Hezbollah sun kaddamar da farmakin ne a yankin tsaunukan Qalamoun a cikin kwanakin da suka gabata.

Kungiyar mabiya shi'ar ta kasar Lebanon ta ce kame muhimman wurare da ke kusa da yankunan kan iyakoki, da ke da tazarar kilomita 50 daga birnin Damascus ya kara musu kwarin gwiwa.

Yankin wani muhimmin wurin shigar da makamai ga mayakan na Hezbolla ne.

Shekaru fiye da uku kenan ake yakin basasa a kasar Syria.