'Matakin soji kadai ba zai kawar da ta'addanci ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen abzinawa sun addabi yankin arewacin Mali

Gwamnatocin kasashen yankin Sahel sun ce daukar matakin soji kadai ba shi ne abin da zai sa a murkushe ayyukan masu tsattsauran ra'ayin Musulunci a Afrika ba.

A cewarsu, dole ne a hada kai domin magance manufofin masu tsaurin akida.

Jami'ai daga Burkina Faso, Mali, Nijar, Chadi da kuma Mauritania sun yi taro a Yamai babban birnin Nijar domin lalubo hanyoyin magance matsalar.

Kasashen da ake kira G5 Sahel -- wadanda galibin al'ummar kasashensu Musulmi ne -- sun sha alwashin daukar matakan dakile yunkurin masu da'awar jihadi na hure kunnen matasa.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a Sahel, Hiroute Guebre Sellasie, wacce ta halarci taron, ta ce kasashen biyar na bukatar wata hanya domin magance ayyukan masu fataucin miyagun kwayoyi da aikata manyan laifuka, wadanda ake kallo a matsayin abubuwan da ke taimakawa ayyukan 'yan ta'adda.