Burundi: Rikici ya barke a Bujumbura

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi ta jin karar harbe-harbe a kusa da gidan talabijin na kasar.

Sojojin da ke goyon bayan Shugaba Pierre Nkurunziza da wadanda ke adawa da shi sun yi arangama a Bujumbura, babban birnin kasar bayan yunkurin juyin mulki.

An yi ta jin karar harbe-harben bindigogi da fashewar abubuwa a kusa da gidan talabijin din kasar.

'Yan sanda sun kai hari a kan gidajen rediyo masu zaman kansu, wadanda suka bayar da rotannin juyin mulki, sannan an tilasta wa akasarinsu rufe gidajen.

Wakiliyar BBC a kasar ta ce wannan arangama ta faru ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin bangaren Babban Hafsan Sojin kasa na kasar da jami'in sojin da ya bayar da rahoton juyin mulkin.

Har yanzu dai Mr Nkurunziza yana Tanzania inda yake halartar taro, bayan ya gaza komawa kasar.