Har yanzu ana cikin rashin tabbas a Burundi

Mutane na cikin firgiji a Bujumbura

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane na cikin firgiji a Bujumbura

Dakarun da ke biyayya ga shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, sun ce sun kwace iko da muhimman gine-gine a Bujumbura babban birnin kasar.

A cewarsu, sun kwato babban filin saukar jiragen sama da kuma kafar yada labarai na kasa.

An ce kura ta dan lafa bayan an tafka kazamin fada tsakanin dakarun da ke biyayya da shugaban kasar da kuma wadanda ke goyon bayan juyin mulki.

Kawo yanzu ba a san inda Mr Nkurunziza yake ba.

Masu goyon bayan juyin mulkin a ranar Laraba suka hana jirgin saman shugaban kasar sauka a filin jirgin saman, abin da ya tilasta masa koma wa Tanzania.

Kungiyar Tarrayar Afrika watau AU ta yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki ta hanyar tashin hankali.

Rikici ya samo asali ne sakamakon yunkurin Mr Nkurunziza na sake tsayawa takara a karo na uku.