Burundi: Menene ya jawo yunkurin juyin mulki ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutune sun yi murnar yunkurin juyin mulki

Wani Janar a sojin Burundi ya ce sun kifar da gwamnatin Shugaba Pierre Nkurunziza.

Hakan ya biyo makonni na zanga-zanga a Bujumbura babban birnin kasar.

Har yanzu ba a san makomar juyin-mulkin ba, a yayin da ake cewa ya makale a kasar Tanzania.

Me ya sa aka yi yunkurin juyin mulkin ?

An soma tashin hankali ne a watan Afrilu, lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya ce zai nemi wa'adin mulki a karo na uku.

Masu zanga-zanga sun bazama a kan tituna inda suka ce tsohon shugaban 'yan tawayen wanda ya shafe kusan shekaru 10 a kan mulki, bai dace ya sake neman wani wa'adin mulkin ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Janar Niyombare da ya jagoranci juyin mulkin

Mutane sun fusata lokacin da kotun tsarin mulki ta ce Mr Nkurunziza wanda 'yan majalisa suka nada a shekara ta 2005, zai iya kara tsayawa takara.

Wasu janar na soji na kallon matakin a matsayin saba wa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 12 ana yi.

Wanene ke mulki?

Babu tabbas a kan haka.

Janar Godefroid Niyombare ne ya sanar da juyin mulkin a rediyo.

A cikin watan Fabarairu ne aka kore shi daga aikin soja bayan da ya shawarci Shugaban kasar ya janye aniyarsa ta neman tazarce.

Janar Niyombare tare da wasu janar biyar jim kadan bayan da suka ba da sanarwar, sai dubban mutane suka kwarara a kan titunan babban birnin kasar domin yin murna.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun da suka ce sun kwace mulki

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce ta dakile yunkurin juyin mulkin.

Menene zai faru a gaba ?

Babu tabbas.

Shugaba Nkurunziza na da matukar goyon baya a kauyuka, kuma ya tafi taron ne Tanzania domin lalubo hanyoyin magance matsalar, kwatsam sai aka yi yunkurin juyin mulki.

Sojojin sun hana shi koma wa gida inda suka kwace iko da filin saukar jiragen saman kasar.

Bangarorin da ke hammaya a sojin sun suma tattaunawa domin kauce wa rikici.

A cikin 'yan makonnin nan, a kalla mutane 40,000 sun tsallaka zuwa makwabtan kasashe bisa fargabar aukuwar tashin hali.

A shekarun baya mutane kusan 300,000 galibi fararen hula ne suka rasu a lokacin yakin basasa a kasar.