Gubar dalma ta hallaka yara 28 a Neja

Hakkin mallakar hoto system
Image caption Gubar dalma ta yi barna sosai a jihar Zamfara

Ma'aikatar lafiya a Nigeria ta ce mutane 28 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar gubar dalma a karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja a arewacin kasar.

Ma'aikatar lafiyar ta ce, kawo yanzu mutane 65 ne suka kamu da cutar, kuma tuni ta fara wayar da kan mutanen da ke yankin game da illolin da ke tattare da cutar gubar dalmar.

Bayanai sun ce wadanda suka mutun duka yara ne da ba su kai shekaru biyar da haihuwa ba.

A shekara ta 2010 ma, cutar gubar dalma ta hallaka yara kusan 400 daga cikin mutane 2,000 da suka kamu da cutar.

Daga cikin alamonin cutar akwai zazzabi da suma da matsalar koda da kuma makanta.