An kashe mutane 42,000 a Brazil a 2012

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amfani da bindiga barkatai ya zama ruwan dare a Birazil.

Wani rahoton da aka fitar kan tashe-tashen hankula a Birazil ya ce kimanin mutane 42,000 aka harbe har lahira a shekarar 2012, wanda shi ne adadin laifuffukan da aka yi da bindiga da ya fi kowanne cikin shekaru 35.

Binciken -- wanda Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnati suka gudanar a kan bayanan da aka samu kwana-kwanan nan ya ce kusan dukkan mace-macen sun faru ne ta hanyar gisan gilla.

Fiye da rabin wadanda aka kashe matasan maza ne 'yan kasa da shekaru 30, an kuma bayyana cewa kashi biyu bisa uku bakaken fata ne.

'Yan majalisar dokokin Birazil suna muhawara a kan wani kudurin doka mai rudani wanda zai rage yaduwar makamai.

Masu gisan gilla da bindiga sun ragu a jihar Rio de Janeiro da Sao Paulo, amma suna karuwa a arewa maso gabashin kasar.

An fi samun tashe-tashen hankula a garin Alagoas da ke arewacin kasar, inda a duk cikin mace-mace dari ake samun 55 na bindiga ne.

Rahoton ya ce jinkirin da ake samu a wajen yanke hukunci da rashin bincike da 'yan sanda ba sa yi da kuma yaduwar makamai na daga cikin abubuwan da ke jawo matsalar.

Rahoton ya ambato cewa "Birazil ta zamo wata al'umma wadda ta lakanci amfani da bindigogi a dukkan wasu al'amura musamman wajen warware matsaloli."

A shekarar 2004 ne aka fara amfani da wata doka da ta haramta daukar bindigogi a bayyane ta ke kuma sa ido kan amfani da bindiga ba tare da izini ba.

Dokar ta tsaurara dokoki kan bayar da izinin amfani da bindiga ta kuma kirkiro da yin rijista ga duk wata bindiga da gwamnati ta bayar da izinin amfani da ita, tare da tsattsauran hukunci ga duk wanda aka kama da bindigar da ba a yi mata rijista ba.