An kama sojin da suka so kifar da Nkurunziza

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

An kama janar-janar na soji a Burundi da suka yi kokarin hambarar da shugaban kasar, Pierre Nkurunziza a Bujumbura, babban birnin kasar.

Janar Godefroid Niyombare -- wanda ya jagorancin yunkurin juyin mulkin -- ya ce dakarun da ke mara masa baya sun mika wuya.

Ya ce, "ina fatan ba za a kashe su ba".

Shugaba Nkurunziza -- wanda ya ce ya koma Burundi daga Tanzania ranar Alhamis -- zai yi wa jama'ar kasar jawabi a kan dambarwar siyasar kasar.

Kakakin shugaban ya ce babu gudu ba ja da baya Mista Nkurunziza zai sake neman shugabancin kasar a karo na uku.

Fiye da mutane 20 ne suka mutu yayin da dubban wasu suka tsere zuwa makwaftan kasashe tun bayan barkewar tarzomar a kasar.