India ta bunkasa kasuwanci da China

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fira ministan India Narendra modi, a wurin taron kasuwanci na India da China a Shanghai

A Shanghai Frai ministan India, Narendra Modi, ya jagoranci sanya hannu kan wasu yarjeniyoyin cinikayya tsakanin India da kamfanonin China, da suka dara na dala biliyan 22. Da yake jawabi ga shugabannin kamfanonin India da na China su 200, Mr Modi, ya ce, India a shirye ta ke da yin harkar kasuwanci.

Yarjeniyoyin sun hada da na fannin tashoshin ruwa da masana'antu da makamashi maras dumama yanayi (renewable energy).

Wannan dai na daya daga cikin ayyuka na karshe da Frai ministan na India zai yi a ziyararsa ta kwana uku a Chinan, wadda aka shirya domin kara dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da suka fi yawan jama'a a duniya.