'Taron kasashen Sahel ba zai yi tasiri ba'

Hakkin mallakar hoto AFP

A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin kare hakin dan adam na ganin babu wani tasirin da taron ministocin cikin gida na kasashen yankin Sahel biyar zai yi.

Shugaban kungiyar Mojen, Malam Siraji Isa, ya ce taron ba zai yi tasiri ba saboda kasashen sun yi taron ne sakamakon umarnin da suka samu daga kasashen Turai.

Ya ce, "taro ne da aka tilasta musu su yi, kuma maudu'in da aka tattauna a taron na kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai bai shafi kasashen ba".

A bayanin karshe na taron, kungiyar ta bayyana cewar zuba jari a kasashen domin aiwatar da ayyukan ci gaba mai dorewa na daga cikin hanyoyi mafi inganci da ka iya taimakawa wajen shawo kan matsalar ta'addanci da kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai.

Kungiyar kasashen ta kunshi kasashen Moritaniya da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi .