APC na fuskantar hadari a majalisa - Shehu Sani

Image caption Shehu Sani ya ce kan 'yan PDP a hade ya ke

Zababben dan majalisar dattijai a Nigeria, Comrade Shehu Sani ya gargadi jam'iyyarsa ta APC cewar tana fuskantar hadari idan har ta ci gaba da yin jinkiri wajen bayyana yadda za a rarraba mukaman siyasa a tsakanin shiyyoyin kasar.

A yanzu haka dai wasu 'yan majalisar wakilai da kuma dattijai suna ta kai-gwauro suna kai mari domin ganin sun samu shugabanci.

A hirarsa da BBC, Shehu Sani ya ce "Tun da aka ci zabe, har yanzu uwar jam'iyyar APC ba ta gayyaci zababbun 'yan majalisa ba domin ta gaya musu manufarta, da kuma abin da ya kamata a zauna a yi domin nasarar sabuwar gwamnati."

"Kan 'yan jam'iyyar APC a rabe yake, wannan kuma zai iya zama illa saboda kamar 'yan PDP kansu a hade yake, hakan zai iya bai wa PDP damar kafa shugabanni a majalisar wakilai da ta dattijai," in ji Sani.

Kawo yanzu dai jam'iyyar APC a hukumance ba ta bayyana shiyyar da take so shugaban majalisar wakilai ko ta dattijai ya fito ba.