Harin Boston: An yanke wa Dhokar hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lauyoyi masu kare Dokhar Tsarnaev, sun ce yayansa ne ya sa shi aikata laifukan

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci a jihar Massachusetts da ke Amurka sun yanke shawarar yanke wa matashin nan dan shekara 21 wanda ya tashi bom, a lokacin wasan tsere a Boston, hukuncin kisa.

Idan dai har lauyoyin Dhokar Tsarnaev suka gaza samun nasara a lokacin daukaka kara, to za a kashe wanda ake tuhumar ta hanyar yi masa allurar guba.

A watan Afrilun shekarar 2013 ne dai Dokhar Tsarnaev da dan-uwansa Termalaen Tsarnaev suka kai harin bom a wurin gasar wasan tsere a Boston, al'amarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Kuma a watan da ya gabata ne kotun ta sami Tsarnaev din da aikata laifin.