Fulani sun fara ficewa daga Ghana

Image caption Fulani makiyaya sun fara ficewa daga kasar Ghana

A kasar Ghana da alamu Fulani makiyaya da sojoji da 'yan sanda suke kora daga jihar Volta a karkashin wani shiri da aka yi wa lakabi da Operation Cowleg sun fara ficewa daga jihar.

Rahotannin da ke fitowa daga kudancin jihar sun ce akalla Fulani makiyaya guda hamsin ne suka fice daga wasu garuruwan yankin tare da shanunsu kimanin dari biyar.

Sai dai kuma hukumomin kasar na cewa korar da ake yi wa fulani ba ana yi ba ne da nufin nuna musu kyama, sai dan wanzar da zaman lafiya tsakaninsu da manoma 'yan kasa.

Hukumomin sun kara da cewa umarnin ficewar makiyayan ba zai shafi fulani makiyaya wadanda suka kasance a kasar kafin samun 'yan kai ba.

Bayanai dai na nuna cewa manoman kasar ta Ghana suna fuskantar mummunan matsin lamba daga fulanin makiyaya, abin da ya janyo asarar abinci mai yawa sakamakon cinye tsirrai da dabbobin makiyayan kan yi.