Fulani za su kai karar Ghana

Image caption Bayan Ghana korafin Fulanin zai hada da abubuwan da ke yi musu a Najeriya da Burkina Faso

Kungiyoyin Fulani a Nigeria sun yi barazanar gabatar da koke gaban kungiyar tarayyar Afrika ta AU da kuma ta raya kasashen yammacin Africa, ECOWAS, kan yadda ake korar Fulani a wasu yankuna na Ghana.

Wani jigo a kungiyar Fulani ta kasa da kasa ta Taftal Fulako, Dakta Garba kawu, ya sheda wa wakilin BBC, cewa nan gaba kadan za su yi taro, su tattara bayanai, sannan su gabatar da kokensu ga kungiyoyin.

A makon da ya gabata ne dai hukumomi a jihar Volta a Ghana suka fara korar daukacin Fulani makiyaya daga jihar, karkashin wani shiri mai suna Operation Cowleg.