Amurka ta ce ta damu da hukuncin Morsi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mohamed Morsi ya sha tuhume-tuhume daga gwamnatin Masar ta yanzu

Amurka ta ce ta damu matuka a kan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke wa hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi, da wasu magoya bayansa su sama da 100.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurkan, ya ce yadda aka gudanar da shari'ar tasu bai dace da yarjeniyoyin duniya da Masar ta amince da su ba da kuma bin doka da ka'ida.

An dai samu Mr Morsi da hannu a laifin fasa kurkuku shekaru hudu da suka wuce a lokacin zanga-zangar juyin juya halin kasashen Larabawa.

Tuni daman Mr Morsi ke zaman gidan yari na shekara 21 bisa laifin tsarewa da kuma azabtar da masu zanga zanga.