Kamaru ta karfafa tsaro a tafkin Chadi

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Gwamnatocin kasashen da ke yankin tafkin Chadi na ta kokarin murkushe kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Kamaru ta karfafa tsaro a yankin Tafkin Chadi, wurin da rahotanni suka ce ya zama matattarar 'yan kungiyar Boko Haram.

An tura dakarun Kamarun ne a shirin ko-ta-kwana domin kare duk wani farmaki a yankin.

An dauki wannan mataki ne kwanaki kadan bayan da kasar Faransa ta jaddada aniyarta wajen tallafa wa Kamarun a yaki da 'yan Boko Haram.

Ana tsammanin kimanin fiye da mayakan kungiyar Boko Haram 300 uku ne suke zaune a dajin Gorifaja da ke kan iyakar Najeriya da tafkin Chadi tun mako guda da ya gabata.

Rikicin Boko Haram wanda aka soma a Najeriya, a yanzu ya yadu zuwa makwabtan kasashe kamar Kamaru, Nijar da kuma Chadi