Abdul'aziz Yari ne shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari zai gaji Rotimi Amaechi

An bayyana gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, a karshen taron kungiyar a babban birnin kasar, Abuja.

Shugaban kungiyar mai-barin-gado, kuma gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi wanda kuma shi ya karanta bayanin bayan taro, ya ce an zabi Abdul'aziz Yari ba tare da wata adawa ba.

Shi dai Yari ya kasance mataimakin shugaban kungiyar a baya. To sai dai kuma ba a zabi sabon mataimakinsa ba a wajen taron.

Kungiyar dai ta fada cikin rikicin shugabanci a watan Mayun 2013 bayan zaben shugabanta, a inda ta rabu gida biyu wato bangaren Rotimi Amachi da na Jonah Jang, gwamnan jihar Plateau.

A hannu daya kuma an zabi Gwamnan jihar Borno, Kasheem Shettima a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin arewa.