Ministocin Turai za su gana a kan 'yan ci rani

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daruruwan 'yan ci ranin Afrika ne ke mutuwa a kokarin su na shiga Turai ko yaushe

A ranar Litinin ne Ministocin kungiyar tarayyar Turai za su yi wani taro a kan 'yan ci rani wanda ake sa ran zasu amince da shirin tarwatsa kananan jiragen ruwan da ake amfani da su wajen satar shigar da bakin haure Turai daga Libya.

Da zarar an amince da shirin, hukumar Turan za ta rika tattara bayanan sirri a kan ayyukan masu safarar bakin hauren da kuma harar jiragensu a teku.

Shugabannin kasashen Turan na fatan za su kai ga daukar wannan mataki na soji a yankin tekun Libya har zuwa gabar tekun na Libya.

Shugabannin Turan na neman amincewar kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a kan wannan shiri.