Ya kamu: Duniya Juyi-Juyi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ana yi wa kasar Guinea-Bissau lakabin cewa ita ce kasa a Afrika da ke kan gaba inda ake hada-hadar miyagun kwayoyi a nahiyar a cikin kusan shekaru goma da suka wuce.

Baya ga cewa ta sha fuskantar juyin mulkin soji ga kuma talauci da ya addabi kasar, amma duk da haka, wasu gungun masu safarar miyagun kwayoyi daga kudancin Amurka na amfani da kasar a matsayin hanyar safarar hodar ibilis zuwa Turai.

'Ya Kamu' wani rahoto ne kashi biya a kan yadda wani matashi ya lalata rayuwarsa da miyagun kwayoyi.

Kashi na farko