Gwajin budurci kan masu son shiga soja a Indonesiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Macen da ba ta da kamun kai ba za ta iya shiga soja ba a Indonesiya

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Indonesiya sun bukaci gwamnatin kasar Indonesia da ta daina tilasta wa mata sojoji da yin gwajin budurci kafin a dauke su aiki.

Kungiyar Human Rights Watch, ta ce gwajin budurcin na "cutarwa kuma wulakanci ne."

Wata kungiyar ma ta dangana shi da azabtarwa.

Rundunar sojin Indonesiya ta tsaya kan bakar ta, a kan gwajin, inda ta ce hakan zai hana shigar mata marasa kintsi aikin soja.

Hukumar 'yan sandar kasar ta sha suka a bara, da ita ma ta bukaci yin wannan gwaji.

Ban da sa baki da kungiyar Human Rights Watch ta yi, akwai kungiyar kula da mutanen da aka azbtar ta kasa da kasa, watau International Rehabilitation Council for Torture Victims (IRCT), ita ma ta yi tsoka a kan wannan dabi'a gabannin wani taron sojin likitoci da aka yi a garin Bali Indonesiya.

Kungiyar IRCT ta bayyana gwajin a matsayin "mummunar take hakkin mata wanda za a iya kallo a matsayin azabtarwa da kuma cin zarafi a dokar kasa da kasa."

Kungiyoyin duka biyu sun yi zargin cewa ana yi wa matan da za su auri mazan sojoji irin wannan gwajin na budurcin kafin a daura aure, amma rundunar sojin ta musa wannan zancen.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A na karrama mata a ranar Kartini a Indonesiya

"Al'ada mara kyau"

Wani kakakin rundunar sojin kasar, Fuad Basya, ya shaida wa BBC cewa gwajin "yana da amfani".

Ya ce shi ya gane dalilin da ya sa wasu 'yan matan ba sa son shiga aikin soja, ya kuma kara da cewa "zai yiwu sun samu hadari, ko sun kamu da wata cuta, ko kuma wasu halaye" wanda ke da nasaba da saduwa da namiji.

"Idan dai dabi'ar su ce, toh rundunar sojin Indonesiya ba za ta karbi masu ire-iren halayen nan ba". In ji Mr Basya.

Kasar ta bukaci 'yan sanda mata da su yi "gwajin budurci".

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Indonesiya na kuma son fara yi wa mata masu son shiga aikin dan sanda gwajin budurci

Hukumar lafiya ta duniya watau WHO, ta ce a ganinta "gwajin budurci" cin zarafi ne ga mata, kuma ba ta da wani tushe a kimiyya.

Akwai dalilai da dama da ke sa ba za a samu fatar budurci (wata jijiya da ke dan rufe bakin farji) a kintse ba in an yi gwaji.

Bayan kakkausar sukar da hukumar 'yan sandan Indonesiya ta sha a shekarar 2014, a kan gwajin da ta tirsasa wa mata masu neman shiga aikin, gwamnatin kasar ta ce ba ta bukatar matan da ke bukatar shiga kwalejin ma'aikatar gwamnati da yin gwajin budurcin.

A farkon shekaran nan an kushe wani shiri a garin Java, da har ya kai ga soke tsarin da ya bukaci 'yan mata a makarantu da sai sun yi gwajin budurci kafin su sami takardar shaidar sakandare.

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mafi yawan al'ummar Indonesiya musulmai ne