Jonathan ya nemi gafarar 'yan Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Jonathan zai bar fadar shugaban kasa a karshen wannan watan

Shugaban Najeriya mai barin gado, Goodluck Jonathan ya nemi gafarar 'yan kasar wadanda ya saba wa cikin sani ko rashin sani a lokacin aikinsa a matsayin tsawon mulkinsa.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wani taron ban kwana da aka shirya masa a cocin da ke fadar shugaban kasa a Abuja, inda ya ce ba da gayya ya aikata kura-kuran ba.

Ya ce "Akwai lokuta da dama da ake yanke hukunci domin amfanin kowa da kowa amma kuma mutane basa gane dalilin hakan."

Shugaba Jonathan ya ce "Ba a ko da yaushe ake samun abu yadda ake so ba; idan har aka jira sai an samu dai-dai, to lallai ba za a iya cimma komai ba. Kuma ko wanne mutum tara yake bai cika goma ba."

Ya kara da cewa, "Saboda haka, a shekaru takwas da na yi a matsayin mataimakin shugaban kasa, da mukaddashin shugaban kasa da kuma shugaban kasa, zan iya cewa ba wanda ba ya kuskure."

Jonathan ya gode wa Allah da kuma wadanda suka kasance tare da shi a lokacin a tsawon wadannan shekaru.