Nijar: An kama dan gwagwarmaya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana ganin kamun baya rasa nasaba da bayyana mawuyacin halin da mutanen yankin tafkin Chadi su ke ciki

A Nijar hukumar 'yan sandan yaki da ta'addanci ta cafke fitaccen dan gwagwarmayar kare hakin dan adam Malam Musa Changari.

Sai dai babu wani karin haske da hukumomin tsaron suka yi dangane da dalilan kama shi.

Amma wasu na kusa da shi na ganin lamarin ba ya rasa nasaba da hirar da ya yi da sashen Faransanci na BBC da kuma rahoton da ya rubuta kan wahalar da mutanen da gwamnati ta tasa daga tsiburan tafkin Chadi na Karamga bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai, suke ciki.

An dai kama Musa Changarin ne a cibiyar 'yan sandan bayan da ya kai wa wani daga cikin masu garuruwa shida a jihar Difa da ke tsare a can abinci.

Hukuma na tsare da masu garin ne bisa zargin kin ba ta hadin kai a yaki da 'yan Boko haram.