Shugaban Burundi ya kori ministoci uku

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an tsaro sun yi harbi a iska a Bujumbura

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya sallami ministoci uku yayinda ake ci gaba da zanga-zanga a Bujumbura babban birnin kasar sakamakon wani yunkurin juyin mulki a makon da ya wuce.

Ya kori ministocin tsaro da na kula da harkokin waje da kuma na cinikayya.

Jamiian tsaro a Bujumbura sun yi ta harbin iska da bindigogi wajen tarwatsa masu zanga-zangar kyamar ta-zarcen shugaba Pierre Nkurunziza.

Matasa da dama ne dai suka datse titunan wasu unguwanni, suna kira ga shugaban kasar da ya sake tunani game da aniyarsa ta neman wa'adin mulki karo na uku.

Mutane fiye da 20 ne aka kashe tun lokacin da aka soma zanga-zanga a watan da ya wuce game da shawararsa ta tsayawa takara a kawo na uku.