Obama ya hana ba wa 'yan sanda kayan soji

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Obama ya ce kayan da 'yan sandan kan yi aiki da su kamata ya yi a gansu a filin yaki

Shugaba Obama ya haramtawa gwamnatin Amurka bai wa 'yan sanda kayan aiki irin na soji, domin hakan na zama barazana ga jama'a da haifar da gaba.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta ce daga yanzu an daina bai wa 'yan sandan motocin silke irin na yaki, da kayan sarki ko kaki irin na rawar daji da kuma manyan bundugogi na harba gurneti.

Shugaba Obama ya bayyana dalilin daukar wannan mataki ne a yayin da ya kai ziyara Camden da ke New Jersey.

Inda ya ce, ''mun ga yadda kayan soji wani lokaci sukan sa mutane su ga kamar wasu dakaru ne na mamaya suka tunkaro su, maimakon jami'an tsaron da su ma wani bangare na al'ummar ne, da ke kare su da kuma yi musu aiki, wanda hakan kan tunzura jama'a da kuma kawo mummunar fahimta. A don haka za mu haramta amfani da kayan da aka yi domin amfani da su a filin daga.''

Shugaba Obama ya bayar da wannan sanarwar ne sakamakon zargin da aka yi cewa, 'yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen kwantar da tarzoma a Ferguson da Missouri a bazarar bara.