IS: 'yan Shi'a za su shiga Ramadi

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Sojin sa-kai na 'yan shi'a za su shiga Ramadi domin fatattakar IS

Dubban sojin sa-kai na 'yan shi'a masu goyon bayan Iran a kasar Iraq sun tunkari Ramadi domin kwato garin daga hannun 'yan kungiyar IS.

Shigar sojin na-sa-kai Ramadi domin fatattakar 'yan kungiyar IS yana nuni da irin mahimmancin da garin yake da shi ga kasar Iraqi.

A satin da ya gabata ne dai 'yan kungiyar ta IS suka kame Ramadi mai tazarar kilomita dari kacal daga babban birnin kasar ta Iraq wato Baghdad.

Ana kallon al'amarin da wani yunkurin 'yan kungiyar na mamaye Baghdad.