WHO za ta kafa asusun yaki da Ebola

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta ce za ta kafa wani Asusun ko-ta-kwana na dala miliyan dari don yaki da cutar Ebola.

Babbar Daraktar Hukumar Margaret Chan, ta bayyana cewa annobar Ebola ta ci karfin Hukumar lokacin da ta barke a shiyyar Afirka ta yamma.

Ta kuma ce abin da aka bukata wajen yaki da ita ya ninka sauran bukatu da hukumar ta saba dawainiyarsu sau goma.

Sama da mutum dubu 11 ne cutar ta kashe bayan bullarta a watan Disamban 2013.

Dr Nasiru Sani Gwarzo Mamba a kwamitin ayyukan gaggawa na yaki da cutar Ebola a hukumar lafiya ta Duniya ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa "asusun zai taimaka wajen daukar matakan da suka dace akan lokacin da ya dace."