An ci gaba da kai harin sama a Yemen

Image caption An samu raba kayan agaji a Yaman a kwanaki biyar da aka tsagaita bude wuta

Rundunar hadin gwiwar sojoji da Saudiyya ke jagoranta ta koma kai hare-hare ta sama kan 'yan tawayen Houthi a Yemen, bayan da yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta kwana biyar tsakanin 'yan tawaye mabiya Shi'a da dakarun gwamnati ta zo karshe.

An kai hare haren ne na yanzu duk kuwa da kwarin gwiwar da wakilin musamman na Majalisar dinkin duniya a Yemen din Isma'il Ould Cheik ya bayyana, na sabunta yarjejeniyar da akalla wasu karin kwanaki biyar.

Wakilin ya ce, ''Mun ga yadda wannan yarjejeniya ta jin kai ta bamu kyakkyawan fata, ta hanyar barin kayan agaji su kai ga al'ummar Yemen, a lokacin da suke matukar bukatar su.''

Duk da dauki ba-dadin da aka samu a wasu wuraren, yarjejeniyar dakatar da wutar ta tabbata.

Rundunar kawancen dai tana aiki ne karkashin hadin gwiwar kasashen Saudiyya da Bahrain da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Kuwet, wadanda suke bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Abdur Rabo Mansur Hadi.