"Na daina zana hoton Annabi" - Charlie Hebdo

Image caption Renald Luz Luzier daya ne daga manyan masu zanen jaridar Charlie Hebdo

Daya daga cikin manyan masu zanen barkwanci na jaridar nan ta barkwanci ta kasar Faransa, Charlie Hebdo, ya ce zai yadda kwallon mangwaro ya huta da kuda, inda zai bar aiki da jaridar.

Renald Luz Luzier, ya ce ba zai iya ci gaba da aikin nasa ba saboda kisan da aka yi wa mutane 12 daga cikin abokan aikinsa a harin da wasu masu tsananin kishin Islama suka kai wa ofishin jaridar a watan Janairun 2015.

Mr Ronald din ne ya zana siffa ko hoton Manzon Allah (SAW) na jaridar bayan wannan hari.

A watan da ya gabata ne, editan ya ce ba zai sake zanen Annabin ba, saboda abin ya daina ba shi sha'awa, kuma zai bar aikin jaridar a watan Satumba.