Boko Haram: Matasa sun kwato makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matasan Tafawa Balewa sun kame manyan bindigogin daga hannun maharan 'yan Boko Haram ne a watan Maris da ya gabata

Matasan karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi sun kwato muggan makamai da dama daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram inda kuma suka mika wa hukumomin tsaro.

Matasan sun karbo makaman ne, wadanda suka hada da bindigogi na hannu da kuma wata zungureriyar bindiga ta kakkabo jirgin sama, bayan da suka fafata da mayakan kungiyar a harin da suka kai yankin a karshen watan Maris.

Mista Ezra Yohanna, shi ne sakataren kungiyar Matasan Tafawa Balewa, ya kuma ce "Sai da muka yi kukan kura kafin muka iya cimma masu tayar da kayar bayan muka kuma kwace makaman da yanzu muka mika wa hukumomin tsaro."

Hakimin karamar hukumar Bogoro Mista Sarautu Damina, na daya daga cikin shuwagabannin al'uma a yankin da suka jagoranci mika makaman ga jami'an tsaro a garin Tafawa Balewa.

Babban kwamandan rundunar mai hidikwata a birnin Jos na jihar Filato, ne ya jagoranci karbar makaman.

A karshen watan Maris ne lokacin zaben shugaban kasa, wasu dimbin mayaka da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hare-hare a wasu yankuna a jihar ta Bauchi cikin kwambar motoci, kafin daga bisa suka gamu da tirjiya a yankin Tafawa Balewa inda aka samu hasarar rayukan mutane da dama galibinsu mayakan, tare da kona motocinsu masu yawan gaske.