Musulmai 'yan Rohingya sun samu sa'ida

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Rohingya na cikin mayuwacin hali

Kasar Thailand ta bi sahun Malaysia da Indonesiya wajen amincewa da bai da mafakar wucingadi da 'yan gudun-hijira kusan dubu Bakwai din nan da suka makale a teku.

Kasar Malaysia da Indonesiya ne suka fara amincewa da ba su mafakar a wata ganawar da Ministocin harkokin wajen kasashen suka yi.

Yarjejeniyar dai ta bai wa kasashen duniya shekara guda domin a samu inda za a tsugunar da su.

Ministan harkokin wajen Indonesiya Retno Marsudi ya yi karin haske kan yarjejeniya " A shirye muke mu samar da taimakon jin kai ga wadanda har yanzu suke a cikin teku."

Ya kara da cewa "A shirye muke mu yi tayin matsugunnin wucin gadi muddun dai za a yi aikin tsugunnarwa da kuma kwashe su a cikin shekara daya."

Galibinsu dai 'yan ci-ranin Musulmi ne 'yan kabilar Rohingya daga Myanmar da Bangladesh.