Ana yi wa sojoji kusan 600 shari'a a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nigeria sun shafe shekaru suna yaki da Boko Haram

Dakarun Nigeria 579 na fuskantar shari'a a kotun soji, a wani mataki na tabbatar da da'a tsakanin sojojin kasar.

Kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kuka-sheka ya tabbatarwa da BBC cewa a ranar Laraba ma an yi zaman kotun soji biyu domin tabbatar da an gaggauta shari'un.

Kanar Usman ya kara da cewa ba duka wadanda ake yi wa shari'a bane ke da hannu a rashin bin umurni a yaki da Boko Haram.

A bara kotun soji ta yanke wa sojoji 72 hukuncin kisa saboda rashin biyayya da yin bore da kuma nura rashin jarumta a yaki da Boko Haram.

An kashe sojoji da dama a rikicin Boko Haram abin da ya sa ake zargin wadansu daga cikinsu da rashin nuna kishin kasa a yakin.

Kananan sojoji a Nigeria sun sha zargin cewa ba a basu makamai domin tunkarar mayakan Boko Haram.