Ma'aikatan NNPC sun fara yajin aiki

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Hedikwatar kamfanin man fetur na Najeriya da ke Abuja

Ma'aikatan kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, sun bi sahun kungiyoyin kwadago na kungiyoyin ma'aikatan mai da kuma iskar gas na kasar watau PENGASSAN da NUPENG wajen yin yajin aiki.

Ma'aikatan PENGASSAN da NUPENG din sun dakatar da aikin hako danyen mai a wasu rijiyoyin mai a yankin Naija Delta mai arzikin mai ne tun a ranar Talata.

Kungiyoyin sun yi zargin cewa ma'aikatar mai ta yi hanzari wajen mika wasu rijiyoyin mai ga wasu kamfanoni, yayin da wa'adin gwamnati ke gab da zuwa karshe.

Sun kuma nemi ministar mai ta kasa da ta soke kwangilar, ba tare da bata lokaci ba.

Kawo yanzu gwamnatin Nigeria ba ta ce komai ba game da wannan batun.