Abin da ya sa mata hawan Keke a Yemen

Hakkin mallakar hoto Bushra Alfusail
Image caption Yaki ya kai mata ga hawan keke a Yemen.

Yaki ya tarwatsa kasar Yemen, kuma labarin da takaici

Wasu 'yan kasar sun yi ta nuna bacin ransu, ba ma a kan fadace-fadace da harin jiragen sama da kuma mummunar karanci abinci da suka shiga ba---amma kan hawan mata keke.

Bushra Al-Fusail wata yarinya ce mai daukar hoto, kuma a tunaninta abin da zai dakile wahalar karancin man fetir da ake fama da shi a Yemen shi ne amfani da Keke.

Ta yi bayanin cewa "A shekara ta 2011, idan ana wahalar man fetir muna samu a wurin 'yan bumburutu".

"Amma yanzu lamarin ya baci har ya kai ba a samu wurin 'yan bumburutun ma," in ji Al-Fusail.

A makon jiya ne Al-Fusail ta kaddamar da yakin nema wa mata manya da yara, damar hawa keke, ta filin dandalin Facebook, inda ta masa lakani da "Mu hau Keke".

Sabanin makwabcinta Saudiyya, matan Yemen suna da damar tuka mota kuma ba abin mamaki bane a ga mace ta na tuki a babban birnin watau Sanaa.

Duk da haka dai, ba a saba ganin mace a kan keke ba, kuma yawancin masu tsatstsauran ra'ayi a Yemen suna ganin ba kamun kai ne ga mace kuma zai nuna siffar jikinta da yawa.

Al-Fusail ta ce "maza na yawo ko'ina a kan keke".

"Sai na yi tunanin menene zai hana mata ma su tuka keke? Tun da bai saba doka ba, kawai yana bukatar karfin zuciya ne".

Kuna cikin rudani a kan Yemen? kuna bukatar karin bayani? Ku saurari mai bayani.

Daruruwan mutane suna nuna amincewarsu na halartar wannan taro a Facebook, amma da ranar ta zo, mata 15 ne kawai suka zo hawan keken watau a ranar 16 ga watan Mayu.

"Yawancin mata a Yemen ba su iya tuka keke ba," In ji Al- Fusail

Ta kara da cewa "Wadanda suka iya kuma suna ji tsoro, wasu kuma iyayensu da mazajensu sun hana su fitowa".

Duk da cewa ba a halarci taron sosai ba, ganin hoton matan da suka je a kan keke a intanet kawai ya sa maza dayawa suka fusata kwarai---inda suka yi ta nuna fushin su a rubuce-rubuce suna kuma dora laifin a kan yakin da kasar ta ke ciki.

An masa lakani a shafin mahawarar da "Toh ga abin da yaki ya janyo mana" inda wasu maza cikin fushi suke tafka muhawara iri-iri, suna cewa "wannan ba da gaske bane, an shirya ne kawai" in ji wani dan kasar.

Wani kuma ya ce "amma wadannan ba mata bane, maza ne suka yi shigar mata."

Al-Fusail ta shaida wa BBC cewa "Na san za su yi maganganu masu zafi, amma ban za ta abin zai basu mamaki har su karyata hotunan ba."

Hotunan mata a kan keke ya bata wa mutane rai a Yemen

Hakkin mallakar hoto Bushra Alfusail
Image caption Hotunan mata a kan keke ya bata wa mutane rai a Yemen.

Wadanda ma ake wa kallon suna cikin daula, sabbanin halin talaucin da mutane miliyan 10 suke ciki a kasar, su ma suna fama da rashin abubuwan more rayuwa.

Al-Fusail da kanta ta samu daruruwan sakonnin batancin da ya sa ta dakatar da shafinta na Facebook zuwa wani dan lokaci, ta ce sai mutane su "huce".

Yanzu dai ta bude shafin na ta, kuma tana shirin tsara wani gangamin tukin keke, na yakin nema wa mata damar tuka keke.

Duk da mutane sun fusata, ta ce yabo a kan aikin da ta yi yana karuwa.

"Mutane na bukatar sauya yanayin tunaninsu" In ji ta, "Ya kamata su daina kallon mata kamar abun zamantakewa, sai in sun bukaci kwana da su ne kawai suke da amfani a garesu".