Boko Haram: Chadi ta tsawaita wa'adin dakarunta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a watan Janairun 2015 sojojin Chadi suka fara fafatawa da Boko Haram

Majalisar dokokin Chadi ta amince da tsawaita wa'adin dakarun kasar a yakin da suke da kungiyar Boko Haram har sai lokacin lokacin da aka sami nasara a yakin.

Sai dai wasu jam'iyyun adawa na kasar Chadin sun ki amince wa da matakin suna masu bukatar cikakkun bayanai kan adadin kudaden da za a kashe da kuma dakarun da za a tura.

Kasar Chadi dai ta bayar da gudunmawar sojoji 2,500 a yakin da Najeriya da makwabtanta ke yi da mayakan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyin jama'a da gidajensu a tsawon shekaru shida.