Yara na cikin mummunan yanayi a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta kudu

Kungiyar Agaji ta 'Save the Children' ta ce wani rahoto a kan kashe-kashen jama'a da fyade da kuma satar kananan yara a Sudan ta Kudu ya yi matukar daga mata hankali.

Fada ya kara muni a tsakanin mayakan Gwamnati da 'yan tawaye magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar.

Kungiyar agajin ta ce kunguyoyi masu dauke da makamai suna ci gaba da daukar yara aiki a matsayin sojoji a jihar Unity inda fadan ya fi muni.

Rahotanni sun bayyana cewar kananan yara maza suna taka rawa wajen kisan fararen hula.

Wasu rahotannin sun ce an kashe yara kanana masu shekaru bakwai.

Kungiyoyin agaji da dama sun janye taimako da suke kai wa sassa daban-daban na kasar saboda tashin hankalin.