Gwamnatin Jonathan ta ki ba da bayanai - Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a rantsar da Buhari a karshen wata

Zababben shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin Jonathan mai barin gado, ba ta bai wa kwamitin da ya kafa, cikakkun bayanai ba game da halin da gwamnatin tarayya ke ciki.

Buhari wanda ya bayyana haka a lokacin da ya karbi rahoton kwamitin da ya kafa, karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Joda, inda kuma ya nuna takaicinsa a kan yadda gwamnati mai shudewa ba ta fahimci gwamnati mai kamawa ba.

"Ba a fahimci gwamnati mai jiran gado ba. Ba muna shirin tuhumarsu bane. Muna kokarin gano ta inda za mu soma ne," in ji Buhari.

Kakakin kwamitin yakin neman zabe na Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ne ya tabbatarwa da BBC hakan a hira ta wayar salula.

A nashi bangaren, shugaban kwamitin karbar mulki, Alhaji Ahmed Joda ya ce a bisa hasashe suka rubuta rahotonsu saboda babu cikakkun bayanai daga gwamnati mai barin gado.

Ana zargin, kwamitin gwamnati mai barin gado karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa, Arc Namadi Sambo da kin ba da hadin kai ga kwamitin gwamnati mai jiran gado, zargin da 'yan jam'iyyar PDP suka musanta.