'Yan Burundi 3,000 na fama da Kwalara

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan gudun hijirar Burundi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kullum ana samun sama da mutane 400 da suke kamuwa da cutar amai da gudawa a cikin 'yan gudun hijirar Burundi da ke Tanzania.

Dubban 'yan gudun hijira ke isa ta kwale-kwale inda suke bi ta wani teku marar kyau a kokarin da suke na tserewa rikicin siyasar da ake yi a a kasarsu.

Ana kuma tsugunnar da su a wuri marar tsafta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kalla mutane 3,000 ne suka kamu da cutar amai da gudawar, yayin da fiye da mutane 30 suka rasa rayukansu.

A bangare guda kuma ana ci gaba da yin bore a babban birnin kasar Bujumbura, domin kin amincewa da tazarce a karo na uku da shugaba Pierre Nkurunziza ke son yi.