Na fi son shinkafa da mai da yaji - Hadiza Gabon

Hakkin mallakar hoto Hadiza Gabon
Image caption Hadiza Gabon na haskakawa a Kannywood

Tauraruwar fina-finan Hausa a Nigeria, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta yi hira da BBC inda ta ba da tarihin kanta da kuma yadda ta tsinci kanta a harkar fim.

A cikin hirar ta bayyana cewar shinkafa da mai da yaji ne abincin da ta fi so, sannan ta yi karin haske kan asalin iyayenta.

Gabon ta ce "A shekara ta 2007 na zo Nigeria inda na yi difloma a harshen Faransanci a jihar Kaduna."

"Na samu nasarori da kyaututtuka da dama, ciki har da kyautar tauraruwar taurari mata da kuma kyautar da gwamnan Kano ya bani har ma kuma da kyautar da na samu a makon da ya gabata a kan fim din Ali ya ga Ali," in ji Hadiza Gabon.

Domin jin cikakken tarihin Hadiza Gabon daga bakinta, sai ku biyo mu a shirin Amsoshin Takardunku na wannan mako.