An kona kotun Shari'a a Kano

Image caption Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso

Rahotanni daga birnin Kano a Nigeria sun ce masu zanga-zanga sun kona babbar kotun shari'a da ke Rijiyar Lemu inda ake sa ran gabatar da wani mutumi da ya yi kalaman batanci ga Annabi SAW.

Wakilinmu a Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce a (yau) Juma'a ne ake sa ran gabatar da Abdul Nyass a gaban kotun na Rijiyar Lemu, bisa kalaman da ya yi a wurin Maulidi wadanda suka tayar da hankulan jama'a da dama a kasar.

Tun lokacin da lamarin ya faru, hukumar Hizbah a Kano, ta kai karar mutumin Kotu domin a tuhumeshi da yin batanci ga Annabi SAW.

Manyan shehunnan darikar Tijjaniyya a Nigeria sun nisanta kansu da kalaman, inda suka ce Abdul Nyass ba ya tare da su.