PayPal zai biya tarar dala miliyan 25

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin PayPal mallakin eBay

Kamfanin manhajar PayPal wadda ake biyan kudin cinikayya ta intanet ya amince ya tara da diyyar dala miliyan 25 a Amurka, bayan an zarge shi da yaudarar masu hada hada da shi.

Wata hukumar gwamnati mai sa ido kan ayyukan kamfanoni ce ta tuhumi kamfanin manhajar PayPal, bayan ya sanya masu mu'amala da shi a cikin wani tsari na nuna sha'awa ga katin biyan kudin ta intanet batare da saninsu ba.

Hukumar ta ce PayPal ya kuma kasa kashe wutar wasu rigingimu da suka shafi biyan kudaden ciniki ta intanet.

Kamfanin na PayPal wanda mallakin eBay ne ya amince ya warware takaddamar amma batare da ya amsa ya yi laifi ba.

Duk da haka dai, ana bukatar alkali ya amince da yarjejeniyar kafin ta zamo halatacciya.