IS ce ta kai hari kan masallacin Shi`a

Mabiya shi`a sun yi cirko-cirko bayan hari Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Jama`a sun dimauta bayan harin kunar-bakin-wake

Kungiyar IS ta ce mayakanta ne suka kai harin kunar-bakin-wake a kan masallacin mabiya shi'a a Saudiyya.

Kungiyar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, wanda ake dogaro da shi wajen samun sahihan bayanai a kan kungiyar.

An dai ba da rahoton cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, wanda aka kai a lardin Gabas, kuma galibin mazauna yankin mabiya akidar shi'a ne.

Mahukunta a Saudiyya sun sha alwashin bankado maharan.

Cikin wani hoton bidiyo da kungiyar ta fitar bara ta yi barazanar kai hari kan mabiya shi'a da ke kasar ta Saudiyya.