Kayan agaji daga Iran zuwa Yemen sun isa Djibouti

Hakkin mallakar hoto tasnimnews.com
Image caption Jirgin ruwan Iran na dakon kaya

Wani jirgin ruwa na kasar Iran dake dauke da kayayyakin agajin jin kai ga jama'ar Yemen ya isa Djibouti, a inda jami'an Majalisar Dinkin Duniya zasu duba kayayyakin dake cikinsa.

Saudiya da kawayenta masu lugudan wuta kan 'yan tawayen Houthi a Yemen suna zargin Iran da taimakawa 'yan tawayen da makamai, zargin da Iran din ta ce ba gaskiya bane.

Iran ta amince ta karkata jirgin zuwa Djibouti ne dominkaucewa arangama da dakarun dake lugudan wuta akan 'yan tawayen Houthi wadanda Saudiya ke jagoranta.

Hukumar hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita za ta karisa da kayayyakin wadanda suka hada da shinkafa da garin filawa da kifin gwangwani da magunguna da ruwan sha da barguna da kuma runfunan tanti.

Dakarun kawancen sun tsananta bincike a kan jiragen ruwa dake shiga Yemen domin hana shigar da makamai da zasu fada hannun mayakan na Houthi.