Hukumar NDLEA tayi wa Kashamu daurin talala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Sanata Buruju Kasahmu ne da fataucin hodar iblis

A Najeriya, jami'an hukuma mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA na yiwa mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na shiyyar kudu maso yammacin kasar kuma zababben sanata a jihar Ogun, Buruji Kashamu, daurin talala a gidansa.

Hakan ya biyo bayan shiga bandaki da wanda ake neman yayi kuma ya kulle kansa a ciki tare da yin barazanar kashe kansa idan dai har jami'an suka karya kofar suka shiga.

Tun dai da misalin karfe 12 na daren jiya Juma'a ne jami'an suka je gidan sanatan amma ba su samu nasarar ido biyu da shi ba.

A ranar Litinin ne za a gurfanar da sanata Buruji Kashamu a gaban kotu bisa zargin yin fataucin hodar Ibilis zuwa Amirka.

Kasar Amirka ce dai ta bukaci a mika mata shi dan fuskantar shari'a.