'Mun ceto mata da yara 20 daga Sambisa'

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mayakan Boko Haram da dama ta kuma ceto wasu mutane 20 daga dajin Sambisa da ke arewa-maso-gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin, Majo-Janar Chris Olukolade, ya ce mata da kananan yara 20 ne sojojin suka ceto daga dajin.

Ya ce duk da irin nakiyoyin da 'yan Boko Haram suka dana akan hanyoyin shiga dajin Sambisan dakarun Najeriya sun samu galaba akansu.

Ya kuma ce sun lalalata sansanoninsu hudu da kuma makamansu da dama.

Amma ya ce sojan Najeriya daya ya mutu a sabilin fashewar wata nakiya, sa'annan kuma an jima fiye da goma raunuka.

Ya ce dukkan sojojin da suka samu raununkan an kai su wuraren kn aura da lafiyarsu.

Karin bayani