Sun dakile harin Boko Haram a Gubiyo

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces
Image caption Sojojin Najeriya sun samu nasarar fattakar 'yan kungiyar boko haram a harin da suka kai Gubiyo a jihar Borno

Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram a Gubiyo jihar Borno. Sun kuma kame motocin da manyan bindigogi

A hirar da wakilin BBC ya yi da wani mazaunin garin ta wayar tarho, ya ce hankula sun kwanta a garin bayan da aka dade ana bata kashi da mayakan Boko Haram da sojoji kafin su fattake su.

Shi ma wani wanda yace dan asalin yankin ne amma yana zaman gudun hijira a Maiduguri, yace an yi hasarar rayukan da dukiya sakamakon kone-konen gidaje da wuraren kasuwanci na mutane da 'yan kungiyar suka aka yi. kuma mutane da yawa sun bazama sun shiga daji.

Kokarin jin ta bakin rundunar sojojin kan wannan labari yaci tura sai dai.

Sai dai a sanarwar da rundunar ta fitar a baya-baya nan, ta ce sojojinta sun samu nasarar tafattakar 'yan kungiyar daga dajin Sambisa a inda tace, ta tarwatsa sasani na karshe a jerin sansanonin 'yan kungiyar dake katafaren dajin har ma ta kubuto karin wasu mata da yara kimanin su 20.