Hukuncin kotu ya wanke dan sanda a Amurka

Dan sandan Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan sandan Amurka

Hukumomi a jihar Ohia ta Amurka sun nemi jama'a su kwantar da hankulansu bayan kotu ta wanke wani dan sanda daga dukkan wani caji da ake yi masa dangane da kisan wasu bakaken fata Miji da Mata a yankin Cleveland shekaru 3 da suka gabata.

Jama'a sun nuna fusata tare da yin bore cikin lumana a birnin bayan an wanke Michael Brelo daga lafin kisan kai na Timothy Russell da Malissa Wiliams.

Dan sandan ya harbe su da bindiga har sau goma sha-biyar a yayinda yake tsaye a gaban motar su.

Karin bayani