APC ta zargi PDP da ruguza Najeriya

Image caption Muhammad Buhari, zababben shugaba mai jiran-gado

Jam'iyyar APC da ke shirin jan ragamar shugabancin Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan mai barin-gado da kokarin wargaza kasar kafin ta mika mulki.

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin PDP mai barin gado da yi wa shugaban kasa mai jiran-gado Muhammadu Buhari zagon-kasa na kin daukar matakai domin kawo karshen dimbin matsalolin da suka addabi al'ummar kasar.

Jam'iyyar dai ta ce wannan shi ne karon farko da wata gwamnati za ta mika mulki ga wata cikin halin matsanancin rashin man fetur da karancin wutar lantarki.

Sai dai ana ta bangaren, Jam'iyyar PDP, a wata sanarwa, cewa ta yi jam'iyyar APC ta saba da karairayi, kuma tana kokarin neman uzuri ne daga al'ummar Najeriyar bisa gazawa wajen cika musu alkawurran da ta yi mu su.