APC ta zargi PDP da bita-da-kulli a Taraba

Hakkin mallakar hoto aisha facebook
Image caption Aisha Jummai Alhassan ce 'yar takarar gwamna a jam'iyyar APC da ta sha kaye a Taraba

Shugabannin jam'iyyar adawa ta APC a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Nigeria, na zargin jam'iyyar PDP da yi wa magoya bayan jam'iyyar bita-da-kullin siyasa.

Ita dai jam'iyyar APC ta yi zargin cewa gwamnatin PDP a jihar na yi wa wasu magoya bayanta kisan mummuke ta hanyar dakatar ko rage musu mukamai a wuraren da suke aiki.

Kuma al'amarin ya fi shafar shugabannin Fulani wadanda aka dakatar daga mukamansu na Ardo.

Tuni dai jam'iyyar ta PDP ta musanta zargin. Ta kuma bayyana shi da wani kagen siyasa.