An tsawaita dokar ta baci a Difa

'Yan gudun hijira a Difa
Image caption 'Yan gudun hijira a Difa

A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ta dauki matakin tsawaita dokar ta baci a jihar Diffa mai fama da hare-haren kungiyar Boko Haram.

Tun da farko gwamnatin ta kafa dokar ne domin ba jami'an tsaro damar ci gaba da karfafa matakan tsaro a yankin.

Wa'adin dokar ta bacin mai ci yanzu dai zai zo karshe ne a ranar 27 ga wannan watan.

Dubban 'yan gudun hijira ne dai 'yan Nijeriya wadanda rikicin Boko Haram ya shafa suka yi sansani a yankin na Difa.

Karin bayani