Rashin mai: An rufe bankuna da makarantu

Image caption Layin man fetur a Abuja

A ranar Litinin ne wasu bankunan a Najeriya suka bayar da sanarwar za su fara rufe ofisoshinsu daga karfe daya na rana a kowacce rana sakamakon matsalar rashin man fetur da take kara ta'azara.

Bankin Guaranty Trust, wanda yana daya daga cikin manyan bankunan kasar, ya ce zai rufe dukkan rassansa da ke fadin kasar saboda rashin isasshen man fetur da za su dinga sakawa a janareto.

Bankin ya fitar da sanarwar ne a shafin sa na Twitter sannan kuma ya aika wa dukkan abokan huldarsa sako ta adireshin email.

Al'amarin dai yana zuwa ne bayan da babban kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cewa rashin man ya fara shafar ayyukansu.

Makarantu ma sun bi sahu

Wasu makarantu ma a Abuja, babban birnin kasar sun ce za su rufe daga ranar Litinin har sai bayan an rantsar da sabuwar gwamnati.

Rashin man dai ya shafi bangarori da dama, lamarin da ya sa 'yan kasar ke fuskantar matsananciyar rayuwa.

Jam'iyyar APC -- da za ta karbi mulki ranar Juma'a mai zuwa -- ta dora alhakin rashin man fetur din kan gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.